Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Liberia Ta Soke Zaben Shugaban Kasar Zagaye Na Biyu


Shugabar Kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf wadda take shirin barin gado
Shugabar Kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf wadda take shirin barin gado

Yau ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasar Liberia zagaye na biyu tsakanin mataimakin shugaban kasar da wani da ya yi fice a wasan kwallon kafa kuma ba'a san ranar da kotu zata amince a yi zaben ba

A jajiberin din ranar zaben fidda gwani a Laberia kotun kolin kasar ta soke zaben, har sai abinda hali yayi, tana nuni da damuwar da aka nuna cewa an tafka magudi a zaben farko.

A jiya Litinin a wani hukunci daya yanke, baban alkali Francis Saye Korkpor, ya ce hukumar zaben kasar na gudanar da ayyukanta “ba yadda ya kamata ba, kuma ba bisa ka’idar doka ba” a yayinda ta shirin gudanar da zaben fidda gwanin, duk da akwai korafe-korafe akan zaben farko da aka gudanar a watan Oktoba. Ba a tsayar da ranar da za a yi zabe zagaye na biyu ba tukunna.

Manyan ‘yan takarar biyu, da suka hada da tsohon ‘dan wasan kwallon kafa George Weah da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai, an shirya zasu kara da juna a zaben fidda gwanin, amma sai dan takarar da yazo na uku Charles Brumskine ya kalubalanci zaben a kotu, yana mai cewa anyi magudi.

‘Yan takarar dai na fafawa ne dominmaye gurbin shugabar kasar Laberia Ellen Johnson Sirleaf, wadda zata sauka bayan da ta kammala wa’adinta biyu. Wa’adin shugaba Sirleaf zai kare ne a watan Janairu mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG