Biyo bayan hukuncin kotun kolin Najeriya dangane da rikicin shugabancin Majami’ar na Kasa.
A jumu’a makon jiya ne kotun kolin ta zartar da hukuncin game da takaddamar shugabancin majami’ar, da aka kwashe fuye da shekaru uku ana tafkawa tsakanin Farfesa Paul Emeka da Mr. Chidi Okarafor.
Shi dai Mr. Okarafor na da’awar cewa shine sahihin shugaban majami’ar Assembly’s of God na kasa baki daya wanda ke da hedkwata a birnin Enugu, a don haka ya nemi lallai Farfesa Paul Emeka, ya sauka ya bashi madafun iko.
Wannan takaddama dai ta kaisu ga tafiya babban kotun taraiyya lamarin da ya zarce har kotun koli, da farko dai babbar kotun ta tarayya ta tabbatar da shugabancin ga Farfesa Paul Emeka, amma kotun daukaka kara ta ce hanyar da aka bi wajen isar da hukuncin a rubuce ga bangaren Mr. Chidi, bata dace da ka’idojin da doka ta shinfida ba
Wannan matsayin dai shine kotun koli ta sake tabbatarwa tare da umarnin cewa lallai a koma domin biyayya ga abinda doka ta gindaya.
Facebook Forum