Ra’ayi ya sha bam-bam tsakanin wakilan majalisa tarayyar dangane da wanke shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki.
A makon nan ne kotun da’a wacce take sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar kan shugaban majalisar dattijan na kin bayyana dukiya ko kadaroinsa ta wanke shi.
Mai magana da yawun majalisar dattijai Senata Sabbi Abdullahi yace “Allah Ya wanke bawansa, amma wadanda tun farko suka hakikance cewa, Bukola yana da laifi ba zasu daddara ba.
A nasa bangaren Suleiman Nazif, ya bayyana farin cikin wannan hukunci, yana mai cewa, suna yiwa “Allah godiya”. Kuma suna tare da shugaban na su dari bisa dari.
Sai dai dan majalisar wakilai Hamma Isa Misau yace, tun fara shari’ar ya hangi cewa akwai matsala, domin akwai alamar karya aka kwantarawa senata Saraki.
Amma Ahmed Babba Kaita, yace akwai bukatar a sake nazarin yadda ake tafiyar da harkokin shari’a, ta yadda za’a gudanar da adalci, maimakon karkata hukunci saboda mukamin mutum
Wani dan jam’iyyar APC, mai mulkin kasar, Khalid Isma’il, yayi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya binciki bangaren shari’a saboda tabbatar da adalci.
Facebook Forum