Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Soke Zaban Emenike A Matsayin Dan Takaran Gwamnan Abia Na APC


Cif Ikechi Emenike
Cif Ikechi Emenike

Wata babbar kotu a jihar Abia ta soke zaban Cif Ikechi Emenike a matsayin dan takaran gwamnan jihar Abia na jam'iyar APC a zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar Alhamis.

A wata karar da wani mai suna Mr Chinedum Nwole da wasu mutum biyu suka shigar, kotun ta ayyana cewa Cif Ikechi Emenike bai da hurumin tsayawa takara tunda yake an dakatar da shi daga jam'iyar APC.

Kotun dai ta kara da cewa da Cif Ikechi Emeniken da kuma Cif Donatus Nwankpa da ke ciyaman jam'iyar a jihar sun saba wa talifi na 9.3 na kundin tsarin mulkin jam'iyar APC ta hanyar tsoma hannu cikin zaben fidda gwanin da aka gudanar.

Toh sai dai kakakin jam'iyyar APC a jihar Abia Honarabul Okey Ezeala ya karyata soke zaben.

Ya ce, ''Ba kotun da ta soke bayyanar Cif Ikechi Emenike a matsayin dan takaran gwamnan Abia na APC a zaben fidda gwanin da aka yi. Wannan yana zuwa ne daga wadanda suka sha kayi a zaben, kuma mun ayyana matsayinmu da zaben wanda ya fi farin jini, kuma shine Cif Ikechi Emenike. Saboda haka ba kotun da ta soke zaben. Kowa na iya biyan jarida ta wallafa masa komai.''

Shi kuwa Cif Donatus Nwankpa wanda aka ambaci sunansa a wannan batun na ganin koda yaushe dole ne doka ta dauki hanyarta.

Ya ce, ''Dole ne a koda yaushe doka ta dauki hanyarta saboda Najeriya tana da kundin tsarin mulki. Ko ni karan kaina an ga laifi na a hukuncin da cewa bai kamata in tsoma hannu cikin zaben ba. Ina kokarin yin nazari ne kan hukuncin in san yadda zan bullo wa batun.''

Yanzu akwai alamun cewa wannan al'amarin ya jefa jam'iyyar APC cikin wani yanayin rudu, kuma sa ido al'ummar jihar Abia suke yi su ga yadda jam'iyyar zata warware batun gabannin zaben 2023.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00
XS
SM
MD
LG