Rundunar ‘yan sanda ta musamman, wadda ke karkashin ofishin Sufeto-Janar na ‘yansandan Najeriya kai tsaya, ta damke wasu gaggan miyagu 30 a jahar Kogi, wadanda su ka dade su na aikata ta’asa a jahohin Kogi da Delta da Edo da Oyo da Ogun kai har ma da babbar birnin tarayya Abuja.
Cikin ayyukan rashin imanin da su ka tabka har da kashe wani bature saboda sun a ganin wanda aka aiko shi da kudan fansa ya boye wasu daga cikin kudin. Wadanda su ka kashe Baturen kai tsaye sun ce shugabanninsu da ke cikin gari a lokacin su ne su ka umurce su da su kashe Baturen muddun ba a ba su kudin fansan da ya kai naira miliyan 70 ba. Su ka ce bayan da su ka gaya ma shugabannin nasu cewa dan aiken ya zake kan bas u kudin fansan da bai kai miliyan 70 din ba sai su ka umurce su da su kashe Baturen, dan kasar Fotugal (Portugal) mai aiki a kamfanin Dangote.
Da ya ke gabatar da miyagun gaban ‘yan jarida a Lokoja, hedikwatar jahar Kogi, Babban Kakakin Rundunar ‘yan sandan Najeriya (PPRO) CSP Moshood Jimoh ya ce tabbatar da cewa wadannan miyagun rikakkun masu laifi ne. Cikin wadanda su ka kashe Baturen da Yahaya Bello daga garin Kuyallon jahar Kaduna, wanda y ace da kiwo yak e yi. Akwai kuma Abubakar Hassan wanda y ace shi dan Kwantagora ne a jahar Naija, wanda ya amsa cewa shi ne ma ya kashe Baturen kai tsaye, ya na mai nadamar cewa lallai ya kashe rayuwarsa shi ma.
Ga dai wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Facebook Forum