Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kirsimeti: Kiristoci A Jamhuriyar Nijar Za Su Yi Addu’o’in Neman Mafita


Wata mai bikin Kirsimeti
Wata mai bikin Kirsimeti

“Halin da ‘yan Nijar ke ciki a yanzu jarabawa ce ta Allah ke nan. A kara hakuri. Abu na biyu lokaci ne da zamu yiwa kasarmu addu’a da shuwagabanimu mu kuma fata Allah ya baiwa Nijar zaman lafiya” a cewar Fasto Benjamin Bernard

A bana mabiya addinin Kirista a jamhuriyyar Nijar zasu gudanar da bukukuwan Kirismetin ne a cikin wani hali na matsin tattalin arziki sakamakon takunkumin da kungiyar ECOWAS ta sanyawa kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a tsakiyar wannan sjekara.

Kiristocin kasar sun bayyana cewa zasu yi amfani da lokacin na Kirismeti domin yi wa Nijar addu’o’in samun mafita inda suka shirya zaman addu’o’i na musamman game da halin da Jamhuriyyar Nijar ta samu kanta a ciki tun bayan juyin mulkin na ranar 26 ga watann Yulin da ya gabata.

“Halin da ‘yan Nijar ke ciki a yanzu jarabawa ce ta Allah ke nan. A kara hakuri. Abu na biyu lokaci ne da zamu yiwa kasarmu addu’a da shuwagabanimu mu kuma fata Allah ya baiwa Nijar zaman lafiya” a cewar Fasto Benjamin Bernard a Maradi.

A Hirar da Fasto Na Allah Oussein dake birnin Yamai, ya yi da Muryar Amurka, yace ranar Kirsimeti “rana ce ta farin ciki da kuma salama ga dukkanin al’ummar duniya ba al’ummar Kirista kawai ba “

Sai dai shirye-shiryen bukin na kirismeti na shekarar bana ya zo dai dai lokacin da al’ummar Jamhuriyyar Nijar ke cikin wani hali na kangin rayuwa, sakamakon takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa kasar, bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan yulin da ya gabata.

Wani mabiyya addinin Kirista, Paul Maria Yawo, ya koka da matsalar da hakan ya jefa shi da sauran al’ummar kasar, ya na cewa “komai yayi tsada a kasuwani sakamakon tashin farashin kayayyaki kama daga kayayyakin hada girki da dai sauransu’’, ya kara da umurtan mata su yi hakuri da abinda mazajensu zasu bayar.’

Paul Agoli wani matashi mazaunin birnin Yamai kuma mawaki tare iyalansa na kallon bukin na Kirismeti a matsayin bukin da ya fi mahimmanci a rayuwarsu.

“A nan muna cikin studio na inda na shirya wata waka ta musamman albarkacin bukin kirismeti mai suna mai ceto na “ in ji shi

Kamar sauran Kiristoci na kasashen Duniya, al’ummar Kirista ta Jamhuriyyar Nijar na ci gaba da shirye -shiryen bukin na kirsmeti da murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu, ranar da ke da matukar mahimmanci ga al’ummar ta Kirista.

A jamhuriyyar Nijar dai mabiya addinin Kirista na gudanar da kyakkyawar mu’amala tare da al’ummar musulmi wadanda suka fi rinjaye a kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG