Kirista da suke ziyara a kasa Mai Tsarki sun yi addu’oi na musamman domin zaman lafiya da hadin kan kasa musamman a arewacin Najeriya inda ake fama da tashe tashen hankali.
A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa ta wayar tarho, shugaban kungiyar hadin kan Kirista reshen jihar Bauchi Rev Shu’aibu Byel yace sakon da suke tafe dashi shine sakon fatar Alheri da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai dabam dabam musamman Kirista da Musulmi a Najeriya.
Yace Allah a cikin ikonsa ya sanya al’ummar kasar a wuri daya, inda ake kabilu dabam dabam da addinai dabam dabam domin cudanya da juna. Yace nufin Allah ne al’ummar Najeriya su zauna tare lafiya domin ci gaban kasa.
Shugaban kungiyar hadin kan kiristan yace sun bar Najeriya a cikin wani yanayi marar dadi kasancewa a ranar da suka tashi aka kai hare haren boma bomai a jihohin Gombe da Bauchi da ya yi sanadin asarar sama da rayuka talatin.
Mahajjata dari biyu da casa’in da bakwai ne daga jihar Bauchi suka sami tafiya kasa Mai Tsarki bana, kuma suna kyautata zaton tashi zuwa Najeriya ranar biyu ga watan Janairu.
Ga cikakken rahoton da Abdulwahab Mohammed ya aiko.