Karamin Ministan Lafiya Dr. Mohammed Pate wanda ya bayyana haka yace gwamnatin tarayya ta tanada isasshen maganin rigakafi sabili da haka babu dalilin da za a ci gaba da asarar rayuka ta dalilin wannan cutar.
Dr. Pate yace yawancin kananan yaran dake kamuwa da cutar, yara ne da ba a yiwa allurar rigakafi ba, saboda haka yayi kira ga iyaye su kara maida hankali wajen yiwa ‘ya’yansu rigakafi, ya kuma nemi hadin kai da goyon bayan malaman addini a wannan fannin.
Kyanda dai cuta ce da ake yadawa ta miyau da aka tofar ko majina da mai dauke da cutar ya fyace a kasa. Alamun cutara sun hada da zazzabi mai zafi da mura da jan ido harshen mutum kuma ya yi fararen kuraje kanana.
An yi kiyasin cewa, kimanin kananan yara arba’in suka rasu ta dalilin cutar kyanda sama da dubu hudu kuma suka kamu da cutar a Najeriya yawancinsu daga jihohin da ake fama da zafi da suka hada da Enugu, Kaduna, Naija Katsina Kebbi da kuma Bauchi.