Dambarwar zaben shekaran 2015, ta raba kawunan al’umar kudanci jihar, kaduna, game da wanda zasu goyawa baya a zaben gwamnan jihar dake tafe a sheran 2015.
Dr. John Dan Fulani, Malamin Jami’a ne kuma dan kudancin jihar ta Kaduna, ya kuma ce akidar da ‘yan kudanci ke da ita na goyawa dan takara daya baya ta riga ta kau, saboda a cewar shi kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
Shi kuma tsohon kwamishinan ilimi, a jihar ta Kaduna, wanda shima dan kudancin jihar ta Kaduna ne Alhaji Suleman Lawal Kauru, yace babu dalilin bijirewa wannan gwamnati ta jihar, Kaduna, saboda ta riga tayi masu komai.
Yankin kudancin jihar Kaduna dake da kannan hukumomi takwas, ya riga yayi suna wajen goyawa dan takara daya baya masamman ma a jamiyar PDP.
Sai dai tun bayan da aka fara tunkaran zaben shekaran 2015, kawuna suka fara rabuwa, saboda wasu ‘yayan kudancin jihar ta Kaduna, na ganin ba zata sake sabuwa a ce su goyawa dan takara daya bay aba tunda suka ce suna da bukatun da suka ce ba’a biya masu ba.