Kwanakin baya ne gwamnatin jihar Kaduna ta kori wasu malaman makaranta su dubu ishirin kana ta yi kememe da kiran da aka yi mata ta mayar dasu aiki.
Dalili ke nan da hadakar kungiyoyin kwadagon Najeriya suka taru a Kaduna da alkawarin fitowa yin gangami yau duk da barazanar da gwamnatin Kaduna ta yi masu na hanasu fitowa ko ta halin kaka.
Gwamnati ta ce ba za ta bari a ta da wani yamutsin da zai haifar da matsalar tsaro ba. Saboda haka, a cewar wakilin Muryar Amurka dake Kaduna da ya zanta da abokin aiki Mahmud Lalo, gwamnatin jihar ta baza jami'an tsaro har zuwa bakin ofishin kungiyar kwadagon dake Kaduna.
Duk da taruwar jami'an tsaron 'ya'yan kungiyar sun fito sun hada hannuwansu suna dauke da kwalaye dauke da rubuce rubuce tare da rera wakoki. Sun kutsa inda jami'an tsaro suka kare suka wuce jami'an tsaron ba tare da tada hankali ba.
Tun daga ofishin nasu suka taka zuwa gidan gwamnati inda suka mika wasikar korafinsu wa Onarebul Saidu Adamu wanda ya kasance mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin labaru domin gwamnan ba ya gari. Ya yi alkawarin mika waskar ga gwamnan.
Ga karin bayani.
Facebook Forum