Frayim Ministan kasar Birtaniya David Cameron ya ce nasarar da ‘yan tawaye su ka yi, su ka shiga Tripoli babban birnin kasar Libiya ta taimakawa juyin juya halin yankin Gabas ta Tsakiya wajen fara kafa demokradiya a yankin.
Mr.Cameron ya fada a yau litinin cewa Birtaniya ta yi amanna, ta taimaka wajen hana yiwa bayin Allah kisan gilla a yankin, kuma ya ce Birtaniya ta na alfahari da rawar da ta taka a cikin juyin juya halin kasar Libiya. Ya ce nan kusa gwamnatin kasar Birtaniya za ta iya fara sakin kadarorin kasar Libiya da ke kasashen waje domin al’ummar kasar ta amfana.
Faransa tace nan gaba kadan shugaban ‘yan tawayen kasar Libiya zai je Paris. Faransa ce kasar da ta fara amincewa da Majalisar mulkin wucin gadin kasar Libiya a matsayin halastacciyar wakiliyar al’ummar kasar ta Libiya.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya yi kira ga shugaban kasar Libiya Moammar Ghadafi da ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda.
A cikin wata sanarwar da ya gabatar da yammacin jiya lahadi bayan da ‘yan tawayen Libiya su ka isa Tripoli, Mr.Obama ya ce Mr.Ghadafi na bukatar sanin cewa ikon kasar ya kubuce ma sa.
Haka kuma Mr. Obama ya ce Amurka za ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya su tallafawa kasar Libiya ta girka tsarin demokradiya cikin lumana, sannan kuma ya yi kira ga Majalisar mulkin wucin gadin kasar da, ta yi la’akari da muradun illahirin al’ummar kasar Libiya.