Kasashen Afirka na daukar matakai akan abin da kwararru ke ganin akwai yiwuwar samun bullar cutar Coronavirus a Nahiyar. Yayin da dangantakar harkokin tattalin arziki da kuma tafiye-tafiye ke karuwa tsakanin kasashen Afirka da China, kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce dole ne kasashen su shirya daukar matakan jinya da kuma kebe wadanda suka kamu da cutar.
A jiya Talata, kasar Habasha ta sanar da cewa ta kebe wasu daliban kasar su uku da kuma wani dalibin kasar China guda daya da suka dawo daga wata jami'a dake Wuhan, a China. An tsayar da daliban ne a lokacin wani binciken tantancewa a tashar jirgen saman kasar, a lokacin ne aka gano su na nuna alamun rashin lafiya, ciki har da tari da mura.
Dr. Munir Kassa, shugaban jami’an ma’aikatar lafiyar Habasha, ya ce kasar ta kuduri aniyar zama da shirin ko-ta-kwana. Tun daga farkon watan Janairu, gwamnatin kasar ta tuntubi Hukumar Lafiya ta Duniya da gwamnatin China akan halin da ake ciki.
A wani karin rahoto, a yau Laraba karon farko aka kwashe 'yan wasu kasashe daga China, yayin da yawan wadanda su ka mutu sakamakon barkewar cutar Coronavirus ya karu zuwa mutane 132, kuma kasashe da yawa na daukar tsauraran matakai akan masu zuwa China.
Wani Jirgin sama da aka yi shatar sa ya kwashe 'yan kasar Japan su dari biyu da shida daga Wuhan, wurin da cutar ta fi kamari, zuwa filin jiragen saman Haneda dake Tokyo a yau Laraba. An kai wasu fasinjoji su hudu asibiti bayan da su ka bayyana cewa ba sa jin dadin jikin su. Jami’an kiwon lafiya na cikin jirgin saman don tantance fasinjojin da kuma sa ido akan su, kafin tashin jirgin da kuma bayan saukar sa.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ce, wani jirgin sama da aka yi shatar sa ya kwashe wasu Amurkawa da ba a san yawansu ba daga Wuhan zuwa Anchorage, a jihar Alaska dake Amurka, inda za a sake yi ma su gwaje-gwaje.
Kasashen Australia, da New Zealand, da Faransa, da Rasha da sauransu, su ma sun sanar da shirin kwashe 'yan kasashensu daga Wuhan a wannan makon.
Facebook Forum