Lauyoyin dan adawar siyasar kasar Zimbabwe Tendai Biti sun ce an maida shi kasar shi ta haihuwa bayan da jami’ai a kasar Zambia mai makwaftaka da su suka ki amince wa da bashi izinin zama a kasar.
Gilbert Phri yace an mika Biti ga hukumar ‘yan sandan Zimbabwe bayan yin watsi da izinin da kotu ta bayar na dakatar da mayar da shi kasar tashi.
Bangaren ‘yan gudun hijiran Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da bayanin cewa, sun damu kwarai da rahoton da suka samu kan kin amincewar Zambia ta baiwa Biti mafaka, da kuma hukuncin da suka yanke na maida shi kasar shi, inda suka bayyana matakin a matsayin karya dokar kasa da kasa.
Biti na daya daga cikin membobi 9 na jam’iyyar Movement for Democratic Change da hukumar ‘yan sandan Zimbabwe ke nema bisa laifin haddasa tarzoma a zaben shugaban kasa da aka gudanar makon da ya gabata, wanda jam’iyyar hamayyar ke ganin anyi magudi domin Shugaba Emmeson Mnangagwa ya samu nasara.
Facebook Forum