Kasar Senegal ta bayyana cewa, ta bankado wata makarkashiyar hambare gwamnatin shugaba Abdulaye Wade ta kuma kama wadanda ake zargi da shirin kai hari a babban birnin kasar. Ministan harkokin shari’a Cheikh Tidiane Sy ya fada a tashar talabijin ta kasar cewa, mutanen da aka kama suna yunkurin kai hari a babbar kasuwar birnin Dakar inda ake samun cunkoson jama’a. An yi wannan sanarwar ne jim kadan bayan wata zanga zanga da dubban mutane suka gudanar a Dakar jiya asabar ta kin jinin shugaba Wade da kuma nuna amincewa rashin ingancin harkokin rayuwa. Masu zanga zanga da dama sun ce gwamnatin tayi zargin kulla makarkashiyar juyin mulkin ne da nufin hanasu zanga zangar. An girka jami’an tsaro a duk fadin Dakar sai dai babu rahoton tashin hankali. An yi zanga zangar ne a dandalin taro dake birnin Dakar ranar cika shekaru 11 da mulkin shugaba Wade. Masu zanga zangar sun ba dandalin lakabi, "Tahrir Sqare" na Senegal, ainihin inda aka yi zanga zanga a Misira watan jiya.
Kasar Senegal ta bayyana cewa, ta bankado wata makarkashiyar hambare gwamnatin shugaba Abdulaye Wade ta kuma kama wadanda ake zargi da shirin kai hari babban birnin kasar
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024