WASHINGTON, D.C —
Kasar Saliyo ce kasa a Afrika ta baya-bayan nan da ta kaddamar da yaki da annobar coronavirus, bayan da aka gano cewa wasu mutane 2 suna dauke da cutar a Freetown, babban birnin kasar na.
Shugaban hukumar yaki da annobar ta kasa, Birgediya Jellie Conteh, mai murabus, ya ce daga ranar Lahadi dokar hana zirga-zirga zata fara aiki tsawon kwanaki uku.
Conteh ya kara da cewa an hana duk wani taron addini, kana gwamnati ta hana shige da fice a kasar ta tashoshin ruwa ko ta jiragen sama.
Bugu da kari Bankin Duniya ya sanar da cewa kasar ta Saliyo, zata samu kudi da suka kai dala miliyan 7.5 daga kudin tallafin da take badawa ga kasashe masu tasowa, domin yaki da annobar coronavirus.