Mr. Bazoum Muhammed yace a matsayinsu na shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS ko CEDEAO ba zasu amincewa sojojin Burkina Faso su rike ragamar mulki ba. Dole su bar 'yan kasar su nada gwamnatin wucin gadi.
Ko menene ake son a yi lamarin yana hannun 'yan Burkina Faso. Su ne zasu zabi abun da suke so ba wai a dora masu wani abu ba alatilas. Amma idan sojoji ne zasu dauki shugabanci kungiyoyin nan biyu na Afirka da Afirka ta Yamma zasu dauki matakan da suka dace. Ana iya dakatar da kasar daga kungiyoyin a matsayin ladabtarwa.
Tun farko shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso Issac Yacoubu ya umurci kungiyoyin su dan dakata su ga abun da 'yan kasar zasu yi. Akan wannan furucin Bazoum Muhammed yace muddin soji ne kan gaba a shugabancin kasar na rikon kwarya ba zasu amince ba.
Yace dadewa akan mulki komin iyawar mutum karshenta bakin jini yake jawowa. Yace Blaise Campaore yayi kuskure da ya nemi ya zarce bayan yayi shekaru 27 yana mulki.
Blaise Campaore shekaru uku da suka wuce shi ya umurci Tanja shugaban kasar Nijer na wancan lokacin ya manta da shirin ta zarce. Amma wai yau sai gashi yayi yunkurin yin abun da ya gayawa Tanja kada yayi. Yace yakamata wannan ya zama daratsi ga duk masu tunanen yin irin hakan.
Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.