Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Mali Ta Nemi Taimakon Soja daga Makwabta


Mayakan 'yan tawaye na kasar Mali
Mayakan 'yan tawaye na kasar Mali
Wani jami’in gwamnatin Faransa yace kasar Mali ta mika takardar neman taimakon soja ga makwabtanta na Afirka ta Yamma, domin ‘yanto yankin arewacin kasar daga hannun ‘yan kishin Islama.

Wakilin Faransa na musamman a yankin Sahel, Jean Felix-Peganon, ya ce kasar Mali ta bukaci kungiyar ECOWAS da ta tura agajin soja domin maido da kwanciyar hankali a kasar, musamman ma domin kwato yankin arewaci.

Jami’in ya fadawa ‘yan jarida cikin daren jiya talata cewar ya samu labarin takardar neman taimakon da Mali ta gabatar din ne a lokacin wata ganawar da yayi da shugaba Blaise Comapore na Burkina Fasso a Ouagadougou.

ECOWAS ta ce a shirye take ta tura rundunar sojoji dubu 3 zuwa Mali, inda masu kishin Islama suke kokarin shimfida yin aiki da irin tasu fassarar ta dokokin shari’ar Islama.
A cikin wannan makon daya daga cikin kungiyoyin ta kwace wani gari, abinda ya kara gusawa da ita ga yankunan da suke karkashin ikon gwamnatin rikon kwarya ta Mali.
XS
SM
MD
LG