Amurka tace ashirye take ta taimakawa Najeriya a fannoni daban daban ciki har da raya kasa da kokatin da shugabannin kasar keyi domin tabbatar da cewa kasar ta ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya.
Jakadan Amurka a Najeriya ya furta hakan a ziyarar da ya kai wa gwamnan jihar Osun Abdulrauf Aregbesola a birnin Osogbo fadar gwamnatin jihar Osun.
Jakadan yace Najeriya nada mahimmanci a wajen ci gaban kasashen duniya inda ya kara da cewa kasarsa zata ci gaba da taimakawa Najeriya a duk hanyoyin da suka dace domin ta ci gaba. Yace hadin kai nada anfani ga kowace al'umma a duk fadin duniya. Saboda haka hadin kan Najeriya nada anfani sabili da haka ne ya ziyarci jihar domin kara fahimmatar kasar.
Yayinda yake yiwa Jakadan maraba, lale, gwamna Aregbesola yace suna jin dadin jagorancin da Amurka ke yiwa kasashen duniya don haka kasar ta Amurka ta kara mayar da hankali da jagorancin domin hana kasashen duniya wargajewa.
Kafin ya isa jihar Osun sai da Jakadan na Amurka ya ziyarci jihar Oyo inda ya sake jaddada matsayin Amurka akan taimakawa Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.
Facebook Forum