Wannan dai wata babbar matsala ce da wadanda ke zaune a gidajen haya ke fuskanta a manyan birane kamar Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, Legas da ke zama tsohon babban birnin kasar, Fatakwal, Katsina da dai sauransu, ke fuskanta inda masu gidajen ke cin karensu ba babbaka a wajen kara kudin haya duk lokacin da suka ga dama.
Lamarin dai a cewar masu hayar na ci musu tuwo a kwarya saboda a mafi yawan lokuta ba su da zabi idan ba su biya kudin da aka yi musu kari ba sai dai su fara neman sabon gida baya ga wahalar da suka sha a baya wajen samun gidan da aka yi karin.
A yayin bayyana nasu korafin, wasu mazauna birnin tarayya Abuja sun shaida wa Muryar Amurka cewa, kamata ya yi gwamnati ta sanya ido a kan lamarin na masu bada gidan haya, don a saukake wa jama’a da ke fama da matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa.
Yawaita kari a kudin haya a manyan biranen Najeriya ba wani sabon abu bane, inda a watan Agustan shekarar 2022 sai da wasu mazauna biranen tarayya Abuja suka gudanar da wani tattaki, don neman gwamnati ta shiga cikin lamarin karin da ake yi don agazawa talakawa da ke zaune a wajen gari da ake yawaita yiwa kari duk da cewa ba karin albashi ake yi musu ba.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf: