Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano, Zaben Kananan Hukumomi Ake Yi Ko Dangwale?


malaman zabe a wani zaben da aka yi a Najeriya.
malaman zabe a wani zaben da aka yi a Najeriya.

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a jahar da ma bangaren Kwankwasiyya a APC mai mulkin jahar duk sun kauracewa wannan zabe.

Yau Asabar 10 ga watan Febwairu, ake zaben kananan hukumomi a duk fadin jahar Kano. Za'a zabi shugabannin kananan hukumomi su 44, da kansiloli masu yawa.

Rahotanni daga jahar sun ce an makara wajen kai kayan zabe da malaman zabe. Wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari, yace har sai bayan karfe daya na rana aka kai kayan zabe a wasu kananan hukumomin.

Amma babban abunda ya lura dashi a wuraren da ya zagaya, musamman a karamar hukumar Doguwa, ba zaben ake yi ba. Yace jami'ai suna baiwa matasa da aka tattaro katunan zabe da tawada, suna ta dangwalawa jam'iyya mai mulki a jahar.

Wakilin na Sashen Hausa yace, ana yin hakanne akan idon jami'an tsaro na 'Yansanda, wadanda bisa al'ada duk lokacin zabe, ake kawo su domin tabbatar da doka da oda.

Zuwa lokacin da muka zanta da Mahmud, bai kai ga jin ta bakin jami'an jahar don jin martanin su gameda abunda ya gani ba, da kuma makarar da aka yi na aikewa da kayan zabe kan lokaci.

Ga tattaunawar da muka yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG