Yayin da aka shiga rana ta biyu da fara amfani da dokar hana zirga-zirgar jama’a a Jihar Kano, wannan doka dai ya sanya ayarin daliban makarantun tsagayu da aka fi sani da almajirai na fita daga Kano zuwa garuruwansu.
Tun a shekaran jiya laraba ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da kafa dokar hana zirga zirgar Jama’a, biyo bayan bullar cutar ta Coronavirus a jihar ranar lahadin da ta gabata.
Baya ga cincirindon mutane a kantuna da shagunan siyar da kayan masarufi a sassan birnin da kewayen Kano, sanarwar sanya dokar ta tilasta wa almajirai komawa garuruwansu.
Hakan dai baya rasa nasaba da dakatar da karatu a galibin makarantu da kuma fargabar da ke zukatan galibin alarammomi da daliban su, na abin da ka iya zuwa ya je saboda halin rudani da wannan cuta ta jefa al’umar duniya.
Dangane da wannan doka ta hana zirga-zirga kuwa alaramma Adamu Abubakar ya ce, dokar ta sanya wasu dalibansa tafiya gida.
Ya ce "daga cikin yaran mu akwai wadanda hankalinsu ya tashi, suka ce suna so za su tafi gida, kuma mun barsu su je gida."
Ya Zuwa yanzu dai, mutum 21 ne aka tabbatar sun kamu da Cutar a jihar ta Kano.
Saurari cikakken rahoton a sauti.
Facebook Forum