Shaikh Abubakar Jibril shi ne limamin da ya jagoranci dubban daruruwan musulmi da suka halarci sallar idi a masallacin dake harabar tsohuwar jami'ar Bayero, Kano.
Dr Muhammad Sani Ayagi yayi karin haske game da abubuwan da hudubar ta kunsa. Yace ta kunshi kira ga al'ummar musulmi da su kayautatawa junasu. Ya fara da su kayautatawa iyali da makwafta da abokan zama da kuma sada zumunci. Ya kuma nuna mahimmanci ranar da fallalar dake tafe da ita da alheri. Rana ce Allah yake gafarta zunubai yake kuma yin kyautar aljanna.
A kaso na biyu limamin ya jawo hankalin al'ummar musulmi akan su hada kansu su tunkari kalubalen da yake fuskantarsu na duniya. Rashin hadin kai shi ya jawo masu matsaloli da yawa.
Wasu da suka halarci sallar sun ce a hakikanin gaskiya sun tarbiyantu da fadakarwar da limamin ya yi masu kuma sun dauki daratsi da fatan Allah zai karbi ibadunsu.
Sarkin Kano Muhammad Sanusi da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje sun bukaci musaulman jihar da su kara kaimi wajen gudanar da addu'o'in wanzar da zaman lafiya a kasa baki daya. Shugabannin biyu sun kuma taya al'ummar musulmi murnar wannan ranar tare da kiran a cigaba da yin anfani da darusan watan Ramadana.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.