Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta tabbatar da cewa kasar ta shiga zango na hudu a matsalar cutar da ke cigaba da yaduwa cikin sauri duk kuwa da kokari da hukumomi a kasar ke yi na yaki da ita .
Rahotanni sun yi nuni da cewa daga ranar 19 zuwa 23 na watan Disamba na wannan shekara ta 2021 jimillar mutanen da suka kamu da cutar covid-19 ya haura mutum dubu 9,500, adadi mafi yawa da aka samu tun bayan bullar cutar a kasar, a jiya Alhamis an samu karin mutane dubu 1,940 da suka kamu da cutar a fadin jihohi 18 ciki har da babbar birnin tarayyar kasar Abuja, hakan na zuwa ne adaidai lokaci da jama’a ke hada-hadar shirin gudanar da bukukuwan krismeti da na sabuwar shekara.
Dakta Adamu Alhassan Umar babban likita ne a Najeriyar ya bayyana cewa sakaci da mutane suke nunawa ga illar cutar shi ya haifar da hawa -hawan adadin masu kamuwa da ita
A wani bangaren kuma ana iya cewa wannan kari da ake samu na wadanda ke kamu da cutar baya rasa nasaba da rashin daukar matakai da nuna tirjiya da mutane ke yi wajen yin allurar rigakafin cutar, ko a ranar Laraba sai da hukumomi a kasar suka kona sama da allurar rigakafin cutar miliyan daya da suka lalace ko wa’adin amfani da su ya wuce.
ko da ya ke babban Darakta a hukumar harkar lafiya a matakin farko a kasar Dakta Usman Adamu ya bayyana cewa allurar da aka kona wadanda ingancin aikinsu ya kare ne amma duk wani allura na rigakafin cutar sai an duba ingancinsa kafin ake ba ko wanne dan kasa.
A cewar Dakta Bulama Garba Abdullahi, Najeriya wacce yawan al’ummarta ya haura miliyan dari biyu, Babban buri da mataki da gwamnatin kasar ke son cimma a yanzu wajen yaki da cutar a kasar shine yiwa kashi 70 na al’umma kasar wato mutane miliyan dubu dari 112 allurar rigakafin cutar na Korona hakan ya sa aka bullo da wani sabon shirin mai taken MASS VACINATION
Alkaluman hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar wato NCDC ya yi nuni da cewa yayin da aka samu sabbin masu dauke da cutar yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai dubu 231, 413, sai dai har yanzu ba’a samu Karin a adadin wadanda suka mutu ba wanda adadin ke kan mutum 2,991, ana kuma kira al’umma kasar da su kiyaye kai daga kamuwa da cutar yayin gudanar da shagugular bikin krismeti da na sabuwar shekara ta 2022.
Saurari sauti cikin Rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.