Shugaban kamfanin kera motocin alfarma na Tesla Elon Musk ya bayyana cewa kamfanin zai fitar da wata shahararriyar motar akori-kura mai amfani da lantarki nan da shekarar 2021. Motar mai suna Cybertruck, Musk ya bayyana hakan ne a wani taron baje kolin motoci da aka yi a birnin Los Angeles.
Farashin motar zai fara daga dala $39,000 ne zuwa sama, kuma karfin batirin motar zai kasance wanda zai tafiya fiye da mil 500 ba tare da ya mutu ba.
Kaddamar da wannan sabuwar motar zai baiwa Tesla damar shiga sahun gaba wanda ya shahara a fagen kasuwar mota a Amurka, inda masu saye ke da burin samun kaya mai nagarta.
Farfesa Erik Gordon da ke sashen kasuwanci a jami’ar Michigan Ross, ya ce yawancin masu sayan motar mai daukan kaya wato akori-kura, su na ta’allaka ne akan nau’i guda, su na la’akari ne da abunda iyayensu su ka amince cewa shine mafi inganci.
Gordon ya ce abun ya na da alaka da dabi’an sabawa da abu, misali wanda ya saba sayen mota kirar Ford ka ce mishi ya koma kirar Chevy Silverado, hakan tamkar ka ce ne ya bar zuri’ar shi.
Motar kamfanin Teslan ta fi kama da irin wanda ake wasa da ita, musamman a lokacin karshen mako.
Shugaban Tesla ya ce motar mai silke ce wanda zata iya jure bindigar hanu wanda bata wuce girman milimita 9 ba.
Facebook Forum