Daya daga cikin manyan kamfanonin wayar salalu ta zamani a duniya, wato Samsung, ya kaddamar da sabuwar wayar sa ta Galaxy S20 mai karfin fasahar zamani ta 5G.
Wayar an inganta ta da sabuwar kyamarar daukar hoto da ke da karfin 100x. Kamfanin ya baje kolin wayar salular ne a wani taro da aka yi a birnin San Francisco.
Kamfanin na fatan cewa sabuwar fasahar wayar da sauri, tsarin kyamara, da kuma girman runbun bayanan wayar zasu iya zama dalilin da zai sa ta iya doke abokan hamayyar ta, kamar Apple da Huawei a cikin kasuwa.
Galaxy S20 ta na da allo inci 6.2 da kyamarori uku a baya, yayin da Galaxy S20 + ke da allo inci 6.7 da kyamarori hudu a baya.
Duka wayoyin su na da kyamarori tare da fasahar habakar gani na 3x, da tsarin dakko bayanai na dijital 30x. Ita kuwa Galaxy S20 Ultra ta na dauke da allo inci 6.9, da tsarin kyamarori hudu a baya.
Wayar kuma na da fasali biyu na tsaye, wanda suka hada da karfin kyamarar da ya kai 108MP, da kyamara wadda fadin ta ya kai 10x.
Facebook Forum