Kimanin mutane sama da billiyan 2 ne a fadin duniya ke amfani da kafar sadarwar zamani ta Facebook a kowace rana. Yanzu haka kamfanin na shirin samar da kudin kansa.
A jiya Talata ne kamfanin ya bayyana shirinsa na samar da nashi nau'in kudin zamani na kimiyya, wanda za’a dinga amfani da su a fadin duniya.
Tsarin zai kara inganta kasuwancin yanar gizo, da kuma kara yawan tallace-tallace a shafin.
Tsarin da kamfanin ke shirin fitarwa tare da hadin gwiwar wasu kamfanoni da suka hada da Paypal, Uber, Spotify, Visa da Mastercard, na iya fuskantar matsaloli, sabo da harsuna da ake da su a fadin duniya, kamar yadda wasu lura.
Kamfanin dai na Facebook da wasu manyan kamfanoni na shafukan yanar gizo, na fuskantar matsin lamba daga majalisar Amurka akan matsalar da ta shafi bayyanan sirrin ma'abota shafukan, amma idan kamfanin ya ce zai samar da nashi nau’in kudi kuwa, hakan zai jefa bankuna cikin hadari.
Mutane za su iya amfani da kudin daga shafinsu na Facebook, wajen amfani da kudin don siyan kowane irin abu na wasu kamfanoni ta hanyar amfani da yanar gizo, kamfanin da aka yi siyayyar wajen su za su cire kudi daga asusun mutun na Facebook din.
Facebook Forum