WASHINGTON D.C —
Kamfanin Cocacola na kasar Amurka kamfanin lemun kwallaba ne da baya bukatar gabatarwa a tsakanin al'umomin kasashen duniya kama daga birane zuwa kauyuka,.
Koda yake kamfanin ya dade a Najeriya, sai dai kuma a wannan karon ta karkashin jagoran kamfanin na reshen jahar Legas, kamfanin ya sayi hannun jari har kashi arba'in cikin dari na kamfanin Civita wanda ke sarrafa mada da lemun jus jus a Najeriya.
Abin tambayo anan shine, ko kamfanin na Cocacola zai bunkasa wannan kamfani na Civita tunda yana da hannun jari a ciki?, wanne irin tasiri zai yi ga matasa da tattalin arzikin kasar?
Ku saurari cikakkiyar hirar a nan...Dandalinvoa.com