Malaman Makarantun Sakandaren sun hadu ne a karkashin tutar hadin gwuiwa na kungiyoyin OTS, OTA da kungiyar Malaman Makarantun Kamaru da Afirka (SECA), inda suka fara yajin aiki yau Litinin.
Matsalolin malaman sakandare biyu ne. Na farko dai ya shafi "bashin da malaman suke bin gwamnati sakamakon jinkiri da aka samu wajen biyan albashi". Shekaru da dama da suka gabata ba a biya malamai albashin da aka dau alkawarin biya kai tsaye da zarar sun fara aiki ba. Hakan ya kan sanya jinkiri shekaru 5 ko ma 10, inji wasu daga cikin su.
Akwai kuma batun wani mataki da aka tsara kuma aka sanya hannu tun daga shekara ta 2000 wanda kawai ake jira a fara aiwatar da dokar da zai shafi kula da jin dadin rayuwar malaman.
Kungiyoyin OTS, OTA da kuma SECA sun kuma yi kira ga malaman sakandare da kada su shiga duk wani biki da ya shafi ranar malamai ta duniya, da za a gudanar ranar Laraba 5 ga wannan watan na Oktoba.
Saurari rahoton Mohamed Ladan: