Jami’ai sun ce da kyar za a yi rana guda ta wuce ba tare da samun rahotannin hare-haren ta’addanci na Boko Haram ko kuma aika-aika masu aikata laifukan kan iyaka da suka hada da gungun ‘yan bindiga da ke kai hari kan fararen hula da namun daji ba a iyakokin kasashen biyu.
Kasashen biyu na tsakiyar Afirka sun ce suna da iyaka da ya kai sama da kilomita 1,100 wanda ke taimaka wa 'yan bindiga da 'yan ta'addar Boko Haram tserewa zuwa Kamaru ko Chadi lokacin da sojojin gwamnati suka fatattake su.
Joseph Beti Assomo, Ministan tsaron Kamaru, ya ce shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, da takwaransa na Kamaru, Paul Biya, sun umurci sojojinsu da su sanya ido tare da kare iyakokinsu daga tashe-tashen hankula da masu tsattsauran ra'ayin IS da gungun masu dauke da makamai ke yi.
Assomo ya kuma ce dubun dubatar 'yan kasar Kamaru da suka tsere daga fadan da ake yi tsakanin masunta da makiyaya a arewacin Kamaru a bara na ci gaba da zama a kasar Chadi.
Gwamnatin Chadi ta ce ‘yan gudun hijirar na kin komawa yankunansu a Kamaru saboda yawan rikici tsakanin makiyaya da masunta.
Daoud Yaya Brahim, Ministan tsaro na kasar Chadi, ya ce dole ne kasashen Chadi da Kamaru su gaggauta dakatar da yawaitar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a kan iyakarsu, tare da kawo karshen satar shanu da kuma kashe giwaye.
Ministocin tsaron sun ce za su kafa shirye-shirye na shugaban kasa don tinkarar wadannan barazana daban-daban a yankin. Sai dai ba su bayyana lokacin da za su fara aikin soji ba.
Dandalin Mu Tattauna