Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kama Wasu Akan Zargin 'Yan Boko Haram Ne Na Kawo Cecekuce


Jami'an Tsaro.
Jami'an Tsaro.

Kwana kwanan nan mahukuntan Najeriya suka kama wasu mutane fiye da dari hudu daga arewacin kasar a jihar Abia ana zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne. Zargin ya soma kawo cecekuce

Daga bisa duk alamu kamawar da jami'an tsaro suka yiwa wasu su 486 a jihar Abia da suka fito daga jihohin arewa yana cigaba da kawo cecekuce.

Akan haka ne ministan watsa labarai na Najeriya Mr Labaran Maku yace gwamnatin kasar ta damu kwarai da gaske dangane da irin yadda ake yada manufofi na kabilanci da bangaranci game da aikin jam'an tsaro.

Kowane dan Najeriya nada 'yancin yayi walwala a koina a kasar amma kuma tilas ne a dauki matakan tsaro idan akwai barazana. Yace matsalar kasar itace abu kadan sai a kawo kabilanci da bangaranci ciki. Yace sati biyu da suka wuce wani gwamnan arewa yace kungiyar Boko Haram na kokarin kai hare-hare a kudancin kasar.

Dangane da wai 'yan Boko Haram ba zasu tafi wani wuri a cikin jerin gwanon motoci ba sai ministan yace mutum ba zai sani ba domin suna iya badda kamanni.

Da yake mayarda martani dangane da matakin da jami'an tsaro suka dauka Dr Bashiru Kurfi shugaban kungiyar dake fafitikan kare hakkin Biladama yace sun kammala shirin gurfanar da gwamnatin tarayya a gaban kotu domin su kalubali gwamnatin. Yace suna son su kare hakkin 'yan arewa Musulmai.

Ga cikakken rahoton Hassan Umar Tambuwal.
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:33 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG