Baya ga mahalarta taron sun nanata bukatar cewa majoji da editoci su kara kaimi wajan tace labarai da rahotanni aka kafofin su, musamman kan al’amurran da suka shafi zanga zanga ko tarzoma a matsayin wani hakki da ya rataya a wuyan sun a tabbatar da doka da oda a cikin kasa.
Sai dai taron ya yi la’akari akan yadda wasu kafafen yada labarai ke wasa da hakkokin ma’aikatan su, lamarin da ke sabbaba ka’idojin aikin jarida a yayin bada rahotanni ko shirye shirye, dan haka mahalarta taron suka ja hankalin mamallaka kafofin yada labarai da manajoji game da bukatar kula da walwalar ma’aikatan jarida yadda ya kamata.
A bangare guda kuma taron ya zaburar da hukumar kula da kafofin labarai ta Najeriya NBC, ta daina saku saku wajan daukar matakin hukunci akan kafofin da basa mutumta ka’idojin yada labarai a kasar, Malam Bashir Muhammad Bashir kwararren dan jarida ne wanda ya kwashe shekaru da dama yana aikin jarida, da sharhi da kuma rubuce rubuce ya yi tsokaci a yayin da ake gudanar da taron.
Ya ce“kwararrun ‘yan jarida sun bayyana cewa a matsayin dan jarida wanda yasan makamar aiki, duk labarin da zai iya haddasa masifa ko rudani, za’a iya aje shi a gefa guda, domin zaman lafiya shine ginshikin kowane irin ci gaba a duniya”.
Domin Karin bayani ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.