Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp, ya bayyana cewa har yanzu a bangaren sa baya jin wani abu, a wasan da za suyi da Barcelona a gasar cin kofin zakarun turai a wata mai kamawa.
A ranar 1 ga watan Mayun bana ne Liverpool zata ziyarci Barcelona, a matakin wasan daf da na karshe na zakarun Turai.
Kocin Kloop yace akwai sauran kwanaki kafin karawar, don haka sun mayar da hankalisune kan neman lashe gasar firimiya na kasar Ingila a bana, wanda hakan zai kawo karshen dako na tsawon shekaru 29 na ganin ta lashe kofin, saboda haka muna bukatar mubi komai a hankali Inji Kloop.
Amma Liverpool ba zata samu karfin lashe Firimiyan ba har sai taga abunda zai kasance ranar Laraba mai zuwa, bayan taga wasan Manchester United da Manchester City, wanda za’a fafata a filin wasa na Old Trafford wanda take bukatar ganin an doke Man City wace take biye da ita a mataki na biyu a saman teburin yanzu haka.
Facebook Forum