WASHINGTON, DC —
A kokarin tabbatar da cewa gagarumin taron tattalin arzikin kasa da kasa da za'a fara yayi tasiri bayan an gama, jiya an yi bikin share faggen taron.
An yi shagulgula a birnin Abuja a shirin share faggen kasaitaccen taron tattalin arziki na kasa da kasa da za'a farashi gadan gadan. Mahalarta taron sun yi muamala tsakaninsu tare da gabatar da jawabai kan hanyoyi da hikimomi da manufofin da za'a bi wurin bunkasa tattalin arziki na al'umma kuma da hada kai na kasa da kasa domin a tabbatar cewa taron zai yi tasiri da cimma manufar da yasa aka kafa shi bayan an kammala.
Bayan jawaban, daya daga cikin masu wakiltar Najeriya a wurin taron Dr Muhammed Fate tsohon ministan kiwon lafiya yayi karin bayani akan mahimmancin taron. A daidai lokacin da aka ce tattalin arzikin Najeriya na yi gaba gaba kuma shi ne ma mafi girma a nahiyar Afirka Dr Fate yace idan an duba talaka bai gani a kasa ba. Yace har yanzu akwai matsaloli dake damun mutanen Najeriya. Cigaban da ake ikirarin an samu a takarda ne. Mutane basu ji a jikinsu ba.
Dr Fate ya cigaba da cewa akwai matsaloli na kwanciyar hankali sabili da tashin hankalin dake faruwa koyaushe. Matasa nada matsalolin neman aikin yi domin su inganta rayuwarsu. Akwai matsaloli na ilimi da kiwon lafiya da ma wasu abubuwa da suka shafi rayuwar al'umma. Yace fata nan shi ne yadda aka ce a takarda tattalin arzikin kasar ya habaka to bari mutanen kasar su jishi a jikinsu nan ba da dadaewa ba
Haka ma Dr Fate yana fatan gwamnatin tarayya da mutanen da suka zo taron zasu fahimci matsalolin da kasar ke fuskanta. Bayan sun tafi tattaunawar da suka yi ya kasance mutane sun ji a jikinsu.
Dangane da cewa lamarin satar daliban Cibok daga jihar Borno kamar yana son ya mamaye tasirin taronsu sai Dr Fate yace koda suka fara taron share faggen dukansu sun sa alamu bakake domin su nuna bakin cikinsu. Yace babu shakka maganar na zuciyar kowa. Yace duk wani mai hankali dole yayi bakin ciki cewa irin wannan lamarin ya faru.
Akan ko matsalar cin hanci da karbar rashawa da rashin wutar lantarki da zaman lafiya zasu sa wasu su yi isgilanci su ki saka jari a kasar yace matsalar da aka fi maida hankali kai shi ne ta shugabanci. Yace shugabanci kuma ba na mutum daya ba ne. Ya kunshi duk mutanen dake rike da wani matsayi a gwamnatance da kuma wasu fannoni. Abun da ake bukata shi ne adalci a shugabanci na kowane matsayi. Idan masu saka jari suka ga adalci a kasa to zasu saka jari ko ma ba zasu samu riba da yawa ba. Yanzu sace yaran da aka yi da kashe-kashen kwana kwanan nan duk wani mai saka jari sai yayi dogon tunane. Fata a nan shi ne tashin hankali zai kwanta domin masu saka jari su samu karfin gwiwar yin hakan.
Idan an samu saka jarin to dole ne a yi adalci wato kada a saka jari a wani yankin wani kuma ya rasa to irin hakan zai raba kawunan mutane. Bukatar kasa ta zama duka al'ummar kasar kawunansu su kasance daya.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.