A karon farko Jirgin da yafi kowane jirgi girma a fadin duniya yayi tashin farko a tashar jirage dake birnin Majave dake jihar California ta kasar Amurka a ranar Asabar da ta gabata.
Jirgin da kamfanin Stratolaunch System Corp ya kirkira wanda tsohon mai kamfanin Microsoft Paul Allen ya fara, tun bayan shigar kamfanin harkar jiragen sama ya samu nasara. Jirgin da akayima suna “Roc” wanda ke da fiffike daya da yayi girman filin kwallo, kana yana dauke da ingina guda shida, sai gangar jiki biyu da yake da.
Tun da misallin karfe 7 na safe jirgin ya tashi, kuma yayi shawagi a sararrin samaniya na fiye da awa biyu, daga bisani ya sauka lafiya a filin jirgin sama na Mojave, dubban mutane sun halarci filin don ganema idon su.
“Wannan abun ban al’ajabi da ban sha’awane” a cewar shugaban kamfanin Jean Floyd, a wani jawabinsa da aka wallafa a shafin kamfanin, sai ya kara da cewar, tashin jirgin ya kara muna kwarin gwiwar inganta jirgin.
Jirgin an kirkireshi ne da tsarin yadda zai dinga harba makamai masu linzami, da kuma daukar wasu jiragen da motocin yaki da nauyin su ya kai nauyin wani jirgin, jirgin kuma yana tafiyar kimanin kilomita 189 cikin awa daya.
Facebook Forum