Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Tucano Da Najeriya Ta Saya Na Kan Hanya Daga Amurka


Jirgin yakin Najeriya (Twitter/Nigerian Airforce)
Jirgin yakin Najeriya (Twitter/Nigerian Airforce)

Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa, rukunin farko na manyan jiragen yakin nan guda 6 samfurin A29 Super Tucano da gwamnatin tarayyar kasar ta sayo daga Amurka, suna kan hanyarsu ta zuwa kasar.

Gwamnatin Najeriya ta sayi jiragen ne ta hanyar wata yarjejeniyar kasuwanci da kasar Amurka, wadda ta ba da kwangilar kudi dala miliyan 329 ga kamfanin SNC, domin kerawa rundunar sojin saman Najeriya manyan jiragen kirar A-29 guda 12 a watan Nuwambar shekarar 2018.

A karkashin yarjejeniyar, ana sa ran duka manyan jiragen yakin su iso Najeriya tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022.

Idan ana iya tunawa, a cikin wata sanarwar da ta fitar a can baya, rundunar sojin saman Najeriya ta ce 6 dana cikin manyan jiragen yakin za su iso kasar a watan Yuli da mu ke ciki, a yayin da kuma za’a sami sauran zuwa watan Disamba.

Kazalika, rundunar sojin saman ta bayyana cewa, ta kammala shirya wuraren ajiye jiragen a barikin soji na Jaji a Jihar Kaduna.

A cikin makwannin baya ma sai da wata tawagar majalisar wakilan Najeriya ta kai ziyara kasar Amurka domin samun bayyanin halin da ake ciki akan kwangilar jiragen da aka cimma yarjejeniyar kasuwancin sayowa tun shekarar 2018, inda tawagar ta nemi amsoshi daga kamfanin kan jinkirin da aka samu na turo su Najeriya.

Karin bayani akan: Air Commodore Edward Gabkwet, Amurka, Jihar Kaduna, Nigeria, da Najeriya.

A cikin wata sanarwa da shelkwatar rundunar sojin saman Najeriya ta fitar, ta bayyana cewa, a ranar Talata ne rukunin farko na manyan jiragen yakin suka baro Amurka kan hanyarsu zuwa Najeriya, kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

Kakakin rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ya kuma ce an riga an shirya bikin rijistar jiragen a matsayin kayan aikin rundunar sojin saman ta Najeriya, inda ya ce a nan gaba kadan kamar cikin watan Agusta wanda za’a sanar da ranar da za a yi bukin da zarar an cima matasaya.

Haka kuma, Gabkwet ya kara da cewa sai da jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, ta kai ziyarar ganawa da matukan jiragen a can Amurka kafin su tashi zuwa Najeriya.

A kan hanyar jiragen zuwa Najeriya, za su bi ta kasashe biyar da suka hada da Canada, Spain, Greenland, Iceland da Algeriya kafin su iso Najeriya kamar yadda kakakin rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana.

Alkaluma daga rundunar sun yi nuni da cewa, an tsara jiragen su bi hanyar da suka bi ne domin kaucewa hanyar tekun Atlantika, irin nisan tafiya da ba a saba bi da jiragen yaki ba.

XS
SM
MD
LG