Biyo bayan umarnin da shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa mayakan Najeriya na gaggauta kawo karshen aika-aikar da ‘yan bindiga ke yi a jihar Sokoto, tuni manyan jiragen yakin sojin saman kasar suka isa jihar.
Kakakin rundunar mayakan saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola ya shaidawa VOA cewa har ma babban Hafsan saman, Air Marshall Sadique Abubakar ya je jihar inda ya duba yadda ake tsara kai farmakin.
Daramola ya ce Babban Hafsan ya duba wuraren da jiragen yakin za su dinga shan mai don fara kai farmakin sannan ya gana da manyan kwamandojin da za su jagoranci kai farmakin.
Wasu daga cikin sakkwatawa da wakilinmu ya zanta da su sun nuna farin ciki da wannan mataki tare da fatan za a gaggauta karya lagon 'yan ta'addan cikin gaggawa.
"Yanzu muka tabbatar da cewa ana yi da gaske don muna ta ganin yadda jirage ke shawagi." In ji Magajin garin Gobir , Alhaji Garba Umar Kamba wanda ya nuna farin cikinsa.
A cikin farkon shekarar nan kawai mutane da dama sun rasa rayukansu a jihar saboda yawaitar kai hare-hare da 'yan ta'adda ke yi a kwannakin nan.
Saurari rahoton a sauti.
Facebook Forum