Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya shaidawa Muryara Amurka cewa an cimma wannan matsayar ne a wani taro da gwamnonin jihohin shida na Arewa ta tsakiya, su ka gudanar a jihar Nasarawa.
Gwamnonin sun yi matsayar samar da rundunar tsaro ta “Community Police” wadda gwamnatocin jihohin ne za su dauki nauyin tafiyar da ayukanta.
Injiniya Abdullahi Sule ya kara da cewa “Ko a ‘yan kwanakin nan sai da muka rantsar da ‘yan sa kai, domin taimakawa wajen samar da tsaro a jihar Nassarawa.”
Ya ce ana kuma ci gaba da tuntubar Sarakunan gargajiya lokaci zuwa lokaci, domin ganin an sanar da hukumomi a kan duk wasu bakin fuskoki da aka gani a cikin al’umma.
To sai dai ya ce suna aiki da jami’an tsaro na gwamnatin tarayya wajen ganin an hukunta duk wadanda aka samu da ayyukan ta’addanci.
Ga cikakkiyar zantawar da Yusuf Aliyu Harande ya yi da gwamnan jihar Nassarawa.
-
Yusuf Harande
Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.