A bayanin da yayi lokacin da yake gabatar da kansa akan dan takarar shugaban kasa jiya a dandalin Eagle Square dake Abuja, Janaral Buhari ya fara ne da cewa yana gabatar da kansa ga duk 'yan Najeriya da kuma Ubangijinsa domin neman shugabancin Najeriya.
Bayan ya bayyana kansa wakiliyar Muryar Amurka ta yiwa wasu fittatun 'yan siyasa tambayoyi akan fitowar Janaral din.
Alhaji Aliyu Na'im Bawan Allah ya zo taron ne daga Fatakwal yace a tafiyar Janaral Buhari da suke gani yanzu suna zaton zai ci nasara Allah kuma zai kawowa kasar canji. Inji shi kowa ya gaji kowa kuma yana bukatar canji. Kamar yadda Janaral din ya fada dole a hada kai a jajirce domin a cimma nasara. Yace wannan karon ba sani ba sabo ne. Yace dole sai an yi gaskiya akan zabe mai zuwa.
Wannan shi ne karo na hudu da Janaral Buhari zai fito takara to an tambayi Sanata Hadi Sidika ko suna da karfin gwiwar samun nasara wannan lokacin. Yace yanzu kan mage ya waye. Sun ga rana. Sai sun tabbatar Buhari yaci zabe.
Ahalin yanzu jam'iyyar APC ce kawai take shirin zaben fidda gwani sabanin matakan da PDP ta dauka inda ta baiwa shugaba Jonathan tikitin tsayawa takara shi kadai ba tare da abokin hamayya ba.
Isa Tafida Mafindi jigo a jam'iyyar PDP yace a siyasar Najeriya fitowar Janaral Buhari daidai ne domin babu yadda za'a yi siyasa babu hamayya. Yace amma a tafiyarsu ta PDP sun ba shugaban kasa da mataimakinsa tikitin shiga zabe ko su bada bahasin yadda za'a yi tafiyar. Yace basu da shakka sun cancanta. A zabe mai zuwa za'a yi lafiya za'a kuma fitar da duma daga kabewa.
Mahalarta taron sun bayyana ra'ayinsu akan Janaral Buhari. Dan majalisa Ahmed Babba Kaita yace sha'awar da Janaral din ya nuna tayi daidai da abun da 'yan Najeriya suke cewa, wato babu wani wanda ya cancanta fiye da Janaral Buhari wanda shi ne kadai zai iya fitar da kasar daga kwamacalar PDP.
Dr Haruna Yarima tsohon dan majalisa yace kowa ya san irin mutumin da Buhari yake. Tsayayyen mutum ne mai rikon amana, mai fadan gaskiya kuma mai tausayin talakawa.
Alhaji Yahaya Muhammed yace Buhari yayi gwamna,yayi minista kuma yayi shugaban kasa amma bashi da ko kwabo a Ingila ko Amurka. Yace abun har yanzu yana daure masa kai. Dalili ke nan da ya fito takara ya roki Allah ya bashi nasara
Ga rahoton Madina Dauda.