Mai shirya fina-finai Steven Spielberg na daga cikin mutanen da suka samu lambar yabo a bikin Golden Globes da ake karrama masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai.
Spielberg, wanda ya shirya “Jaws,” “Schindler’s List” da “Saving Private Ryan”, ya lashe lambar yabo ta darekta da ya fi kowa da fim dinsa “The Fabelmans,” wanda shi ya lashe fim din ya fi ficce a bikin, wanda aka yi a karo 80 a jihar California.
Wannan ita ce lambar yabo ta uku ta Golden Globes da Spielberg mai shekaru 76 ya lashe .
A baya, ya taba lashewa da fim dinsa na “Schindler’s List” da “Saving Private Ryan.”
A daya gefen kuma, Darekta Martin McDonagh, ya lashe lambar yabo ta wanda ya rubuta labara mafi inganci yayin da Colin Farrell ya lashe lambar yabo ta jarumin da ya fi fice a fannin wasannin barkwanci.
A fannin jarumin da ya fi fice a wasan dirama, Austin Butler ya lashe lambar yabo saboda rawar da ya taka a fim din fitaccen mawaki “Elvis.”
Ita kuwa Cate Blanchette jarumar da ta fi iya wasan kwaikwayo da fim din “Tar.”
Angela Basset, ta kafa tarihi, inda ta zama ta farko daga kamfanin shirya fina-finai na Marvel da ta lashe lambar yabo ta Golden Globes da fin din “Black Panther: Wakanda Forever.”
Wannan nasara ta sa ta zama jaruma ta farko da ta lashe kambun na Golden Globes daga kamfanin shirya fina-finai na Marvel.
Ita kuwa Ke Huy Quan, ta ya lashe Jaruma mai taimakawa a fim ne da rawar da ta taka a fim din “Everything Everywhere All at Once.”
Baya ga haka, an karrama jarumi Eddie Murphy da lambar yabo ta Cecil B. DemMille.