Ban da tsaro da aikin noma Janaral Buhari zai inganta aikin hako ma'adanai domin samar ma matasa aikin yi.
A taron gangamin fafitikar neman zabe da ya gudanar a jihohin Filato da Nasarawa Janaral Buhari ya nanata cewa matsalolin tsaro, rashin aikin yi da cin hanci da rashawa su ne suka yiwa 'yan Najeriya katutu.
Yace idan Allah Ya yadda sun kama madafin iko zasu tabbata an samu tsaro da zaman lafiya a duk fadin kasar. Sabili da haka ya umarci masu saurararnsa su jefa kuri'arsu amma su kasa su tsare su raka har sai an bada sakamako. Zai kuma hana cin hanci da rashawa kuma kudin da suka gare za'a gyara makarantu da asibitoci kana a taimakawa masu kananan sana'o'i.
Mai masaukin baki gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura ya bukaci mutanen jihar su fito kwansu da kwarkwatarsu domin su zabi APC. Duk wanda ya je wurin zabe ya tabbatar APC tayi nasara. Gwamnan yayi alkawarin kyautata rayuwar al'umma.
Mutane sun bayyana abubuwan da suke son gwamnatin Buhari tayi masu, wato kama daga ba nakasassu ilimi da kwato 'yan matan Chibok.
Ga rahoton Zainab Babaji.