Yayin da Najeriya ke fama da karuwar nau’ukan matsalolin tsaro da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali mabambantan al’ummomi, Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce za a sake fasalin matakan tsaron Najeriya ta yadda za a iya dakile irin wadannan fituntunin idan sun taso.
Janar Buratai ya ce Rundunar Sojin Najeriya ba za ta lamunta da yadda wasu ‘yan tsagare ke yawan sace-sacen jama’a, ciki har da shugabannin al’ummomi, su na kashewa da zummar tayar da fitina ko kuma wani dalili ba. Janar Buratai ya yi wannan kashedin ne lokacin da gwamnan jahar Filato, Barrister Simon Lalong ya je yin ta’aziyyar rashin Manjo-Janar Idriss Alkali, wanda wasu ‘yan tsagerun yankin Dura Du da ke jahar Filato su ka mar kisan gilla.
Janar Buratai ya bayyana cewa daga cikin motocin da aka zakulo daga cikin wani kududdufin da ke Dura Du yayin binciken, akwai ma wadda tun a 2013 aka jefa ta. Ya ce ba a gudanar da bincike kan matar da aka jefa tun a 2013 din a lokacin da abin ya faru ba har maganar ta shiririce. Ya ce wannan wata manuniya ce ta irin gazawar da bangaren tsaro ya yi. Ya ce kisan Janar Idriss ya sa bangaren tsaron Najeriya ya farga matuka.
Facebook Forum