Yau Laraba dubban mutanen da su ka hada da jami’an gwamnati da mambobin majami’u dabam-dabam ne su ka halarci jana’izar mutane 44, da harin bam din kunar bakin waken ranar Kirsimeti ya hallaka su a Majami’ar St. Theresa da ke unguwar Madalla da ke kusa da babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.
Tuni dai kungiyar nan mai tsattsauran ra’ayin Islama ta Boko Haram, mai fafatukar kakaba tsarin shari’ar Musulunci a fadin Nijeriya ta dau alhakin kai harin.
Cikin wadanda suka halarci bison har da Limamin Kiristan Fadar Shugaban Niejriya wanda ya wakilci Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya a wurin jana’izar.
Saurari: