Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Ta yi Kira Ga Kasashe Da Suke Kungiyar G-20 Su Kara Zuba Jari A Afirka.


Shugabar Jamus Angela Merkel
Shugabar Jamus Angela Merkel

Shugabar kasar Jamus Angela Maerkel Ce Tayi wannan kiran, da nufin dakile korarar 'yan-ci-rani zuwa Turai

Shugabar kasar Jamus Angela Merkel, ta yi kira ga manyan kasashen duniya masu arzikin masana’antu na G20 da su bullo da sabon tsarin zuba jari da bada taimako a Afrika. Ta yi wannan kiran ne, kafin ta karbi bakwancin taron kasashen na G20 da za a gudanar a watan gobe idan Allah ya kaimu. Wannan shiri da ake kira Markel plan, ya bukaci Karin zuba jari a Afrika, don rage kwararan 'yan gudun hijira daga nahiyar zuwa Turai.

A wannan mako ministan harkokin wajen Jamus Gerd Muller, ya bayyana fargabar cewa idan ba a dau mataki ba, 'yan gudun hijira daga Afrika da zasu shigo Jamus zasu kai miliyan dari.

A saboda haka, shugabar ta Jamus ta sha alwashin zuba jarin dalla miliyan 335 da zai ja hankalin masu zuba jari daga kasashen waje zuwa Afrika, kana zata yi kokarin shawo kan sauran kasashe 19 na kungiyar G20 da zasu halarci taron kolin, da su kara kudurta taimakawa tattalin Afrika mai fama matsaloli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG