Shugaban Gambia Yaya Jammeh, wanda ya sha kaye a zaben kasar da aka yi a watan jiya, ya amince zai mika mulki kuma ya bar kasar, kamar yadda sabon shugban kasar mai jiran gado Adama Barrow ya fada.
Shawarar da Jammeh ya yanke na mika mulki ya biyo bayan ziyarar da shugaban Guinea Alpha Conde, da kuma takwaran aikinsa na Mauritania Mohammed Ould Abdel Aziz, suka ka kai masa ziyara jiya jumma'a, suka shawo kansa cewa ya mika mulki kuma ya fice daga kasar, ko kuma ya fuskanci matakin soja.
Shugaba Adama Barrow, yayi rantsuwar kama aiki ne a ofishin jakdancin kasar dake Senigal ranar Alhamis, bayan da ya kasa gudanar da haka a Banjul, fadar kasar Gambia.
Rahotanni sun ce, an shimfida jar darduman nan ta karama a tashar jirgin sama dake Banjul, wanda yake nuna alamun Yaya Jammeh, yana shirin barin kasar.
Haka nan a jiya Jumma'a, babban jami'in tsaron kasar, Ousmane Badije yayi mubaya'a ga sabon shugaban kasar.
Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka ECOWAS suka ce sun baiwa Jammeh har zuwa tsakar ranar Jumma'a agogon yankin, yayi murabus.
Bayan wannan wa'adin ne shugaba Jammeh ya nemi karin lokaci na sa'o'i hudu.
Shugaban kungiyar ECOWAS Marcel Alain de Souza, yace shugaba Alpha Conde, zai baiwa shugaba Jammeh damar ya mika mulki cikin ruwan sanyi. "Idan haka ya faskara, zamu tilas tashi ta ko halin kaka,"
Kwamitin sulhu na MDD tun farko ya amince da matakin sojan, kuma ya amince da Adama Barrow a zaman sabon shugaban kasar.
Ranar Alhamis, kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta gwamnatin Obama, John kirby, yace Amurka tana goyon bayan matakin da rundunar sojin ta ECOWAS ta dauka "domin mun fahimci cewa, dalilin shine daidaita lamari na zaman dar-dar, domin mutunta burin 'yan kasar ta Gambia."