Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyun siyasa a Guinea - Bissau sun yi watsi da tsarin zaben sojoji


Sojojin da su ka yi juyin mulki a Guinea-Bissau kenan ke tashi daga wani taron da su ka yi
Sojojin da su ka yi juyin mulki a Guinea-Bissau kenan ke tashi daga wani taron da su ka yi

Wani rukunin jam’iyyun siyasa a Guinea –Bissau ya yi watsi da

Wani rukunin jam’iyyun siyasa a Guinea –Bissau ya yi watsi da shawarar sojojin da su ka yi juyin mulki a wannan satin ta wai a kafa gwamnatin wuccin gadi kafin a gudanar da zaben Shugaban kasa a karshen wannan watan.

Jam’iyyun sun gana da sojojin a jiya Asabar, kuma ana sa ran cigaba da tattaunawa a yau Lahadi. Jam’iyyun siyasan sun gwammace amfani da kundin tsarin mulkin kasar wajen warware dambarwar siyasar.

Juyin mulkin sojin da aka yi ranar Alhamis ya janyo tangarda ga yakin neman zaben Shugaban kasa, tare da jefa wannan kasa ta Yammacin Afirka cikin wani sabon rudami.

Hukumar ta soji ta yi gaba da fitaccen dan takarar Shugaban kasa kuma tsohon Firayim Minista Carlos Gomes Jr. da kuma Shugaban kasa na wuccin gadi Raimunda Pereira bayan sun kai farmaki a gidajensu.

Jam’iyyarsu Gomes, Jam’iyyar Afirka ta ‘yanto Guinea-Bissau da Cape Verde (PAIGC a takaice), ba ta halarci ganawar ta jiya Asabar ba, a maimakon haka ma sai ta fito da wata takardar bayani inda ta ke kiran da a sako Gomes tare da yin tir da juyin mulkin da sojojin su ka yi.

Al’ummomin duniya ma sun yi tir da kwace mulkin da sojoji su ka yi a wannan kasar ta Yammacin Afirka ta Guinea Bissau, ana sati biyu kafin gudanar da zaben fidda gwani ran 29 ga wata na Afirilu.

A nan Amurka ma a jiya Asabar, kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Mark Toner ya fitar da takardar jawabi wadda ta yi tir da abin da ta kira “yinkurin wasu sojoji na kwace mulki da karfin tsiya da kuma kawo cikas ga halaltacciyar gwamnatin farar hula ta Guinea-Bissau.”

XS
SM
MD
LG