WASHINGTON, DC —
Jam’iyyun adawar Junhuriyar Nijer sunce suna da ja kwarai gameda ikrarin nasarorin da gwamnatin shugaba Issoufou Mouhammadou tace ta samu a mulkinta na shekaru ukku. Da yake magana da wakilinmu Abdoulaye Mamane Amadou a birnin Niamey, daya daga cikin ‘yan adawar, Doudou Rahama, yace magangannun da ministan watsa labarai kuma shugaban jam’iyyar PNDS mai mulki Bazoum Mouhamad yayi a jiya, ba gaskiya bane:
Jam’iyyun Adawar Nijer Sun Maida Murtani ga Jam’iyya Mai Mulki
- Aliyu Mustapha
![Shugaba Mouhammadou Issouffou, Junhuriyar Nijer](https://gdb.voanews.com/4c796a35-c96f-46bd-b24e-05b0785553e5_cx0_cy13_cw0_w250_r1_s.jpg)
Jam’iyyun adawa sun kalubalanci ci gaban da gwamnatin PNDS tace ta samu a shekaru ukku