A karshen makon da ya wuce ne, Gwamna Ameachi yayi takarar neman shugabancin kungiyar Gwamnonin Najeriya inda ya yi nasara akan Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang. Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Goodluck Jonathan dan jam’iyyar ta PDP ya goyi bayan Gwamna Jonah Jang ne, kuma faduwar Mr. Jang bai yi wa shugaban dadi ba.
Dama a baya-bayanne ne, aka fara ganin alamun rashin jituwa tsakanin Gwamnatin kasa da Gwamna Ameachi, inda har aka hana jirgin Gwamnan tashi, aka janye jami’an tsaron dake kare magoya bayanshi, kuma aka kori wasu shuwagabannin PDP wadanda ake tunanin magoya bayan Ameachin ne, daga jam’iyyar.
Kafin fitowar sanarwar dakatar da shi, Gwamna Ameachi ya tsaye akan bakansa cewa shine zababben shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya.
Wakilin Muryar Amurka a babban birnin Abuja ya rawaito cewa sabuwar jam’iyyar APC na sha’awar jawo Gwamna Ameachi domin ya shiga jam’iyyar.