Jami’an tsaron Jumhuriyar Nijar sun cafke miyagun kwayoyi a garin Konni, garin dake kan iyaka da tarayyar Najeriya.
Mahukuntan Nijar din sun gudanar da bikin nuna lodin miyagun kwayoyin ne a Birnin Konni da aka kiyasta kudinsu ya wuce sefa miliyan talatin da bakwai.
Malam Hamisu Shuda, Daraktan ‘yansandan gundumar Konni, yace kwayoyin da suka kama yanzu sun kai dubu dari biyu baicin dubu hamsin da suka kama makon da ya gabata.
Magajin garin Konni, Dr. Usman Sumaila, yace da yake kamun ba shine na farko ba, suna kira ga gwamnatin kasar da ta kara taimakawa jami’an tsaro da kayan aiki wadatattu don suci gaba da wannan aikin nasu.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Facebook Forum