Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Jihar Oyo Sun Ce Sun Shiryawa Zabe


A Yayinda zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalissu a Najeriya ke karatowa, jami’an tsaro a jihar Oyo, sun yi kashedi tare da bayyana irin matakai ko shirin da suka yi don tabbatar da cewa an yi zabukan lami lafiya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo, Abiodun Odude ya ce za su yi amfani da karfin doka akan duk wadanda ke neman tada zaune tsaye ko aka kama da harsasai ko makamai, zasu yabawa aya zaki.

Shi ma jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron farin kaya da ake kira Civil Defence, Olusegun Oluwole, ya bayyana irin matakan da zasu dauka don ganin komai ya tafi daidai a lokacin zabe, da kuma kare rayukan mutane da dukiyoyin jama’a.

Mr. Oluwole ya kuma bukaci jama’a su taimakawa jami’an tsaro don ganin an gudanar da zabukan lafiya.

Kwamandan runduna ta biyu ta sojojin Najeriya dake Ibadan, Manjo Janar Ogundele Azinta, ya ce bisa umurnin hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, rundunar ta biyu ta tsara wasu aikace aikace don tabbatar da tsaro a lokacin zaben na shekarar nan ta 2019. Kwamandan ya kuma bukaci jama’a su fita su kada kuri’un su ba tare da wata shakka ba.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG