Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta bayyana cewa gamayyar Jami’an tsaro sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga sama da 200 a jihar.
Jihar Nejan dai na fama da matsalar ‘yan bindiga da suka addabi jama’a da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa sannan da kona gidajen jama’a da kuma kisan mutane.
A wani taron manema labarai kwamishinan kananan hukumomi da masarautu da kuma tsaron cikin gida na jihar Nejan, Mr. Emanuel Umar ya ce gamayyar jami’an tsaron da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya na civil defence da kuma ‘yan banga sun tafka wani gumurzun da ya sa suka samu nasarar halaka wadannan ‘yan ta’adda a garuruwan Babban Lamba dake yankin karamar hukumar Kontagora da kuma Kundu ta karamar hukumar Rafi. Amma kuma suma biyu daga cikin jami’an tsaron sun rasa rayukkansu.
hakan na zuwa ne a daidai lokacin da al’umar jihar Nejan ke kara nuna damuwa akan halin zaman zullumi da fargabar wadannan ‘yan fashin daji.
Alhaji Awaisu Giwa Kuta wanda shugaban al’umma ne a jihar Nejan ya ce kadan ya rage ‘yan bindigar su aukawa birnin Minna fadar Gwamnatin jihar.
Bayanai dai sun nuna cewa a yanzu haka akwai daruruwan garuruwa da suka zama tamkar kufai a wasu yankuna na kananan hukumomin Rafi, da Shiroro, da kuma karamar hukumar Mariga, a sakamakon yadda wadannan ‘yan fashin daji suka tarwatsa al’ummomin dake zaune a cikinsu
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: